Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026, yayin gangamin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi, inda ya nemi al’umma su sake zaɓen Tinubu a 2027.
Ya ce gwamnatin tarayya na gudanar da manyan ayyukan tituna, gadoji da sauran shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziki, ciki har da babbar hanyar Calabar zuwa Abuja da za ta ratsa jihohin Ebonyi, Benuwe, Kogi da Nasarawa, da kuma gadar Ndibe da za ta haɗa Ebonyi da Cross River.
- ’Yan sanda sun kubutar da mutum biyu da aka yi garkuwa da su a Yabo
- EFCC ta horas da manyan jami’anta kan tattara shaidu da gabatar da ƙara a kotu
- Wike ya yi alƙawarin magance ƙarancin albashin kansilolin Abuja
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce gwamnati na tallafa wa manoma ta hanyar raba taki, shirin FarmerMoni da sauran tallafin noma, baya ga tallafin kuɗi da horar da matasa kan sana’o’in zamani.
Ya ƙara da cewa an ƙarfafa tsaro a yankin, tare da fara aiki a cibiyar horas da sababbin sojoji ta Amasiri-Edda a Jihar Ebonyi.

A nasa jawabin, Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya ce jihar ta amfana da sauye-sauyen tattalin arziki da ayyukan tituna na gwamnatin Tinubu, inda ya yi alƙawarin cewa jihar za ta ba shugaban ƙasar kashi 80 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen 2027.
Sai dai ya buƙaci gwamnatin tarayya ta samar da layin wutar lantarki mai ƙarfin 330kV domin inganta wutar jihar.

A yayin ziyarar, an kuma naɗa Shettima sarautar gargajiya ta Aka Ekpuchi Ọnwa, wadda ke nufin “Hannu ba zai iya rufe wata ba”, a matsayin girmamawa ga hidimarsa da kuma alaƙar zumunci tsakanin al’ummar Arewa da Kudu maso Gabas.