Dakarun sojin Najeriya sun kama wani mutum da ɗansa bisa zargin alaƙa da ƙungiyar ’yan ta’addan Lakurawa a Jihar Sakkwato, yayin da suka kashe wani da ake zargin ɗan ta’adda ne a Jihar Katsina.
An kama mutanen biyu ne a ranar 11 ga Nuwamba, 2026, a wani samame da dakarun Operation FANSAN YAMMA suka kai a dajin Bauni da ke ƙaramar hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato, bisa bayanan sirri.
Sanarwar da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Kyaftin Tamuno Sinivie, ya fitar ta bayyana cewa waɗanda aka kama, uba da ɗansa ne, kuma ana zargin suna da alaƙa da ƙungiyar Lakurawa.
- Majalisar Wakilai ta amince da kudurori uku kan asibitoci, ɓarkewar zazzabin cizon sauro da OPay
- Majalisar Wakilai ta amince da kudurori uku kan asibitoci, ɓarkewar zazzabin cizon sauro da OPay
- UNICEF ta bukaci shugabannin duniya su cika alƙawarin kare haƙƙin yara
A yayin samamen, sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, harsasai uku, gidan ajiye harsashi da kuma kuɗi Naira 9,760.
A halin yanzu, waɗanda ake zargin suna hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
A wani samame da aka kai ranar 10 ga Nuwamba a Bada’u Gora, ƙaramar hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, dakarun sun kashe wani ɗan ta’adda bayan sun yi masa kwanton ɓauna bisa bayanan sirri kan shirin kai hari ga al’ummar yankin.
Bayan kashe shi, sojojin sun ƙwato bindiga AK-47 guda ɗaya, harsasai shida, babur da wayoyin hannu guda uku.
Rundunar ta ce ba a samu asarar rai ko rauni a ɓangaren dakarunta ba, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai kan ayyukan da ake zargin na ta’addanci ne.