Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da wasu kudurori uku na gaggawa da suka shafi ƙarin kuɗaɗen gudanar da asibitocin manyan makarantu, ɓarkewar cutar zazzabin cizon sauro a Jihar Zamfara da kuma matsalolin da suka shafi shirin kamfanin OPay na shiga kasuwar hannayen jari ta New York.

A zaman majalisar na ranar Laraba, ’yan majalisar sun buƙaci ƙara yawan kuɗaɗen da ake warewa asibitocin koyarwa na tarayya da cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya, tare da samar da wani shiri na musamman domin gyara ababen more rayuwarsu da ɗaukar ƙwararrun ma’aikatan lafiya.

Dangane da ɓarkewar zazzabin cizon sauro a Zamfara, majalisar ta buƙaci tura jami’an lafiya cikin gaggawa zuwa ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi, tare da samar da magunguna, kayan gwajin cutar da gidan sauro mai maganin kashe sauro.

Ta kuma nemi gudanar da bincike kan yaɗuwar cutar da tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa.

A wani ɓangare kuma, majalisar ta umarci shugabanninta su tattauna da hukumomin da abin ya shafa kan matsalolin ƙa’idoji da aka ruwaito suna kawo cikas ga shirin OPay Digital Services Limited na shiga kasuwar hannayen jari ta New York.

Majalisar ta ce ya kamata a ɗauki matakan diflomasiyya da na hukumomi domin kare muradun kamfanonin da aka kafa a Najeriya da ke neman damar shiga kasuwannin hada-hadar kuɗi na ƙasashen waje.

An miƙa batun asibitoci da na zazzabin cizon sauro ga kwamitocin majalisar da abin ya shafa domin ƙarin bincike da mataki, yayin da aka bai wa shugabannin majalisar alhakin bin diddigin batun OPay tare da gabatar da rahoto cikin makonni biyu.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *