Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta shawarci direbobi da sauran masu amfani da hanyar Kano zuwa Wudil da su yi taka-tsantsan, sakamakon bikin kammala horo da za a gudanar wa ɗaliban runduna ta takwas ta Kwalejin Horar da ’Yan Sanda da ke Wudil, ranar Asabar, 21 ga Nuwamba, 2026.

Rundunar ta bayyana cewa za a gudanar da bikin ne daga ƙarfe 7:00 na safe zuwa 2:00 na rana a filin fareti na kwalejin.

Bikin zai kasance na kammala horon ɗaliban, waɗanda za a naɗa su jami’an ’yan sanda masu muƙamin Mataimakan Sufeto na ’Yan Sanda (ASP).

Ana sa ran manyan baki, jami’an gwamnati da na ’yan sanda, iyalan waɗanda suka kammala horon da sauran jama’a za su halarci bikin, lamarin da ka iya haifar da cunkoson ababen hawa da na jama’a a hanyar Kano zuwa Wudil.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar 20 ga Nuwamba, rundunar ta buƙaci direbobi su guji tuƙi cikin ganganci, wuce-gona-da-iri, gudu fiye da ƙima da kuma yin wucewar da ba ta dace ba.

Ta kuma buƙaci su bi dokokin hanya da umarnin jami’an tsaro, tare da guje wa yin fakin a wuraren da ba su dace ba.

Rundunar ta ce ta tura jami’an kula da zirga-zirgar ababen hawa da tawagogin sintiri zuwa muhimman wurare, mahadar hanyoyi da wuraren da za a karkatar da ababen hawa a kan hanyar Kano zuwa Wudil da cikin garin Wudil.

Ta kuma shawarci matafiya su tsara tafiyarsu tun da wuri, su yi amfani da wasu hanyoyi idan ya zama dole, tare da barin hanya a buɗe domin motocin gaggawa da ayarin motocin hukuma.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gode wa jama’a bisa fahimta da haɗin kai, tare da buƙatar su ba jami’an da ke bakin aiki haɗin kai domin tabbatar da gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali.

Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *