Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gudanar da bincike mai zaman kansa kan tsarin fasahar AI da take shirin amfani da shi wajen sarrafa sakamakon zaɓen 2027.
Atiku ya ce amfani da fasahar AI wajen sarrafa sakamakon zaɓe ba tare da isasshen bayani da matakan kariya ba, na iya jefa amincewar jama’a ga tsarin zaɓe cikin haɗari, musamman idan fasahar ta iya jinkirta, ƙin karɓa ko kawo cikas ga aika sakamakon zaɓe.
A cikin takardar ƙorafi da ya aikewa shugaban INEC, a madadin jam’iyyar ADC da wasu masu ruwa da tsaki a harkokin dimokuraɗiyya, Atiku ya buƙaci hukumar ta bayyana bayanan fasaha da yadda tsarin yake aiki, ciki har da bayanan da aka horar da AI da su, ƙa’idojin gano saɓani da sunayen masu ƙirƙirar tsarin.
- NAOWA ta tallafa wa zawarun sojoji 800 wajen samun hannun jari a matatar Dangote
- INEC ta buƙaci matasan Kudu maso Kudu su kare dimokuraɗiyya gabanin zaɓen 2027
Ya kuma buƙaci ƙwararrun masana tsaro ta yanar gizo, wakilan jam’iyyun siyasa da masu fasahar zamani daga ƙungiyoyin farar hula su samu damar gudanar da bincike kan tsarin kafin atisayen zaɓe na ƙasa baki ɗaya da aka shirya ranar 28 ga Nuwamba, 2026.
Atiku ya nuna damuwa kan haɗa AI da tsarin tantance takardu wajen haɗa tsarin tantance bayanan masu zaɓe da na duba sakamakon zaɓe na INEC, yana mai cewa ya kamata a bayyana wa ’yan Najeriya yadda fasahar za ta yi aiki.
Ya kuma yi gargaɗin cewa matsalolin hotuna, rubutun hannu ko takardun sakamako da suka lalace ba su kamata su zama dalilin hana karɓar ingantaccen sakamakon zaɓe ba.
Atiku ya buƙaci INEC ta samar da tsarin duba sakamakon da AI ta nuna akwai matsala, tare da bayyana waɗanda za su gudanar da binciken, yadda za a rubuta hukuncinsu, yadda za a sanar da jam’iyyun siyasa da kuma hanyar da za a bi wajen ƙalubalantar kuskuren tantancewa.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya kuma ce AI ya kamata ya zama kayan aikin gudanarwa ne kawai a ƙarƙashin kulawar mutane, ba tare da ikon goge, sauya ko hana sakamakon zaɓe fitowa ba, yana mai buƙatar INEC ta tabbatar da matsayin Form EC8A da aka cike kuma aka sanya wa hannu a rumfar zaɓe, tare da buƙatar Majalisar Ƙasa ta gayyaci shugabannin hukumar domin bayyana tsarin da matakan kariya.