Shugabar Ƙungiyar Matan Jami’an Sojin ta Najeriya (NAOWA), Dakta Safiyyah Hassan Shaibu, ta jaddada aniyarta na inganta walwala, kiwon lafiya da kuma ƙarfafa tattalin arzikin iyalan sojoji, musamman zawarun waɗanda suka rasu suna bakin aiki.

Ta bayyana hakan ne yayin ziyarar girmamawa da ta kai wa Kwamandan Rundunar Sojojin Tankokin Yaƙi ta Najeriya, Manjo Janar Umar Bichi Abubakar, a jihar Bauchi, ranar 16 ga Nuwamba, 2026.

Dakta Safiyyah ta ce manufar shugabancinta ita ce gina ƙungiyar NAOWA mai haɗin kai da ƙirƙire-ƙirƙire, wadda za ta ƙarfafa iyalan sojoji ta hanyar dogaro da kai da samar da hanyoyin samun abin dogaro mai ɗorewa.

Ta ce ƙungiyar ta mayar da hankali kan walwalar iyalai, ci gaban ilimi da samar da damarmakin ci gaba.

Ta bayyana wasu ayyukan da ƙungiyar ta gudanar a fannin kiwon lafiya, ciki har da gyara da samar da kayan aiki a sashen gaggawa na Asibitin Sojoji da ke Legas, da kuma bayar da na’urorin jinya guda 10 na cutar kansa da na’urar gwajin jini ta zamani ga Asibitin Ƙasa da ke Abuja.

Ta kuma ce aikin kafa cibiyar wankin ƙoda a Asibitin Rundunar Sojoji da NAOWA da ke Abuja ya kusa kammala.

Shugabar NAOWA ta kuma bayyana cewa ƙungiyar ta taimaka wajen samar da hannun jari kyauta, aƙalla guda 20 ga kowace zawara, ga zawarun sojoji sama da 800 a rassan ƙungiyar daban-daban, ta hanyar shirin sayar da hannun jari na matatar Dangote.

Ta ce shirin na da nufin ƙarfafa samun kuɗaɗen shiga da samar da damarmakin tattalin arziki ga zawarun waɗanda suka mutu suna bakin aiki.

A nasa jawabin, Manjo Janar Umar Bichi Abubakar ya yaba wa shugabar NAOWA kan ƙoƙarinta na inganta rayuwar iyalan sojoji, tare da alƙawarin ci gaba da tallafa wa ƙungiyar wajen cimma manufofinta.

Ziyarar ta ƙunshi sanya hannu a littafin baƙi, musayar kyaututtuka da ɗaukar hotunan haɗin gwiwa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *