Kochi Isa Ladan Bosso.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Abia Warriors ta naɗa gogaggen mai horar da ‘yan wasa ɗan Najeriya, Coach Dr. Isa Ladan Bosso, a matsayin sabon babban kocinta, bisa yarjejeniyar shekara guda.

Bosso ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar daga hannun Imama Amapakabo, wanda ya yi murabus sakamakon rashin kyawun sakamakon wasannin da ƙungiyar ta samu a baya-bayan nan a gasar Premier ta Najeriya (NPFL).

Naɗin nasa ya zo ne a wani muhimmin lokaci ga ƙungiyar da ke zaune a garin Umuahia, wadda a halin yanzu take matsayi na 19 a teburin gasar NPFL bayan buga wasanni 13. Wannan matsayi ya sanya ta cikin haɗarin faɗawa rukunin ƙasa.

Ana sa ran tsohon kocin ƙungiyar matasa ta Najeriya, Flying Eagles, zai yi amfani da ƙwarewarsa da dabarun horar da ‘yan wasa wajen farfaɗo da ƙungiyar tare da ceto ta daga yankin masu fuskantar koma wa rukuni na biyu.

Da yake amsa tambaya daga manema labaru, Bosso ya amince cewa aikin da ke gabansa ba ƙaramin ƙalubale ba ne, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa haɗin kan dukkan masu ruwa da tsaki a ƙungiyar zai taimaka wajen cimma nasara.

“Tabbas babban aiki ne mai matuƙar wahala, amma idan aka yi la’akari da jajircewa, sadaukarwa da ƙwarewar dukkan waɗanda abin ya shafa, ta fuskar fasaha da gudanarwa, za a iya cimma wannan buri,” in ji Bosso.

Gogaggen kocin ya zo da tarin ƙwarewa da ilimi zuwa ƙungiyar Warriors, bayan ya jagoranci ƙungiyoyi daban-daban da kuma tawagogin ƙasarsa a tsawon rayuwarsa ta aikin horarwa.

Babban aikinsa na farko shi ne tabbatar da daidaiton ƙungiyar, inganta sakamakon wasanninta da kuma dawo da kwarin gwiwar ‘yan wasa, yayin da Abia Warriors ke ƙoƙarin ficewa daga yankin masu fuskantar faɗuwa daga gasar.

Yayin da aka ba shi wa’adin shekara guda, Bosso na fuskantar babban aikin gaggawa na samar da sakamako mai kyau da kuma tabbatar da cewa ƙungiyar ta ci gaba da kasancewa a gasar firimiya ta ƙasar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *