Hukumar ta bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da ƙungiyoyin matasa a yankin Kudu maso Kudu, wanda wani ɓangare ne na shirin da take gudanarwa a yankuna shida na ƙasar domin ƙarfafa zaman lafiya, sahihancin zaɓe da kuma shigar matasa cikin harkokin dimokuraɗiyya.
Kwamishinan Zaɓe na Jihar Akwa Ibom, Farfesa Anugbum Onuacha, ya yi kira ga matasa da sauran masu ruwa da tsaki da su taka rawa wajen tsara yadda za a gudanar da zaɓe, tare da jaddada muhimmancin gaskiya, ƙwarewa da kuma shigar da kowa cikin tsarin zaɓe.
- Rashin isassun tsare-tsare da damammaki suna cikin manyan kalubalen ci gaban wasanni a Najeriya
- HOTUNA: NNPC ta karrama mata 20 da suka yi fice a harkokin makamashi
Ya tabbatar da cewa INEC ba ta da jam’iyya ko ɗan takara, kuma tana amfani da darussan zaɓukan baya wajen inganta ayyukanta.
Haka kuma, Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) da Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) sun buƙaci matasa su guji zama kayan aikin siyasa wajen haddasa tashin hankali, tare da amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa sahihan bayanai da wayar da kan jama’a.
Sun kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya, haƙuri da kuma balagar siyasa.
A yayin taron, jami’an INEC sun gabatar da bayanai kan shirye-shiryen zaɓen 2027, laifukan zaɓe da hukuncinsu, amfani da na’urorin BVAS da sabbin fasahohi, da kuma rawar da matasa za su taka wajen yaƙi da bayanan ƙarya.
An kuma ƙirƙiri ƙungiyar WhatsApp domin ci gaba da tattaunawa, wayar da kan matasa da kuma musayar ra’ayoyi tsakanin hukumar da wakilan ƙungiyoyin matasa.