Shugaban Hukumar yi wa Ƙasa Hidima ta NYSC, Birgediya Janar OO Nafiu, ya yaba wa rundunar sojojin Najeriya ta 9 Brigade bisa tallafi da haɗin gwiwar da take bai wa shirin NYSC a Jihar Legas.
Nafiu ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ban-girma da ya kai hedikwatar rundunar da ke Legas, inda kwamandan rundunar, Birgediya Janar AO Owolabi, ya tarbe shi.
Shugaban NYSC ya ce rundunar na taka muhimmiyar rawa wajen samar da yanayin da ya dace domin gudanar da shirye-shiryen hukumar yadda ya kamata, tare da taimaka wa matasan da ke gudanar da hidimar ƙasa a rundunar.
- Najeriya ta kammala gasar Olympics na matasa na Dakar 2026 da tarihi mai kyau
- ’Yan sanda sun ceto fasinjoji 10 da aka yi garkuwa da su a Ogun
A nasa jawabin, kwamandan 9 Brigade ya yi wa tawagar maraba, sannan ya yi wa shugaban NYSC bayani kan ayyukan rundunar, shirye-shiryenta da matakan da take ɗauka wajen ƙarfafa tsaro da zaman lafiya a yankin da take kula da shi.
Wani muhimmin ɓangare na ziyarar shi ne tattaunawar da shugaban NYSC ya yi da masu yi wa ƙasa hidima da ke rundunar, inda ya yaba da gudummawarsu wajen ci gaban ƙasa tare da ƙarfafa musu gwiwar kasancewa masu ladabi, jajircewa da kishin ƙasa.
Ziyarar, wadda mai kula da NYSC a Jihar Legas da wasu manyan jami’an hukumar suka raka shi, ta ƙara jaddada haɗin gwiwar rundunar sojoji ta 9 Brigade da NYSC wajen bunƙasa matasa, haɗin kan ƙasa da inganta ayyukan hidimar ƙasa.