Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta sanar da sallamar Michael Carrick daga matsayin kocin farko na tawagar maza.
Carrick ya koma ƙungiyar ne a watan Janairun 2026, inda ya jagoranci ta zuwa matsayi na uku a gasar Premier League ta kakar 2025/2026, bayan samun nasara a wasanni 12 cikin 17 da suka rage a kakar.
- Najeriya ta kammala gasar Olympics na matasa na Dakar 2026 da tarihi mai kyau
- AFCON 2027: ’Yan wasan Super Eagles 24 sun kammala haɗuwa a Uyo, don karawa da Tanzania
Ƙungiyar ta ce a wannan lokacin Manchester United ta samu maki mafi yawa a gasar idan aka kwatanta da sauran ƙungiyoyi, amma rashin kyakkyawan farawa a kakar bana ya sa shugabanninta suka yanke shawarar sauya koci domin cimma burin da suka sanya a gaba.
A sanarwar da ta fitar, Manchester United ta yaba da jajircewa, ƙwarewa da ƙwarewar jagoranci da Carrick ya nuna, tana mai cewa zai ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun tsoffin ’yan wasanta.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa za ta naɗa sabon koci na dindindin cikin gaggawa domin maye gurbinsa.