Babban sakatare a Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Ƙasa ta Tarayya, Dr. Binyerem C. Ukaire, ya wakilci Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, a taron ƙasa kan harkokin tallace-tallace na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.
An gudanar da taron ne a ranar 12 ga Nuwamba, 2026, inda Ukaire ya haɗu da Darakta-Janar na Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Najeriya (ARCON), Dr. Olalekan Fadolapo, da shugaban Global Alliance for Public Relations and Communication Management, Farfesa Justin Green.
- ’Yan sandan Imo sun horas da jami’ai 500 kan ƙwarewa da mutunta haƙƙin jama’a
- ’Yan sandan Imo sun horas da jami’ai 500 kan ƙwarewa da mutunta haƙƙin jama’a
Sauran manyan jami’an da suka halarci taron sun haɗa da Darakta-Janar na Hukumar Kula da Yaɗa Labarai ta Rediyo da Talabijin (NBC), Charles Ebuebu; Darakta-Janar na Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), Ali M. Ali; da Babban Sakataren Majalisar Kula da Aikin Jarida ta Najeriya, Dr. Dili Ezughah.
