Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce ya bar ƙasar Turkiyya zuwa Tehran bayan kammala ziyarar aiki da kuma halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi karo na 31 (COP31).

A saƙon da ya wallafa, Pezeshkian ya bayyana cewa ya gana da shugabannin ƙasashen Turkiyya, Iraƙi da Brazil, da kuma firaministocin Pakistan, Armenia da Norway.

Ya kuma ce ya gana da shugaban yankin Kurdistan na Iraƙi a yayin ziyarar.

Shugaban Iran ya bayyana cewa tattaunawar tasu ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa dangantakar diflomasiyya, faɗaɗa haɗin gwiwa da kuma tattauna muhimman batutuwan da suka shafi yankunansu da duniya baki ɗaya.

Sai dai Pezeshkian bai bayyana ƙarin bayanai kan yarjejeniyoyin da aka cimma ko takamaiman matakan da aka ɗauka yayin waɗannan ganawa ba.

A cewarsa, ziyarar ta ƙare ne bayan ya halarci taron COP31 tare da gabatar da jawabi, kafin ya nufi Tehran.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *