Stella Archibong, wadda ta kasance ’yar takarar mataimakiyar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) a Jihar Cross River, ta fice daga takarar tare da bayyana goyon bayanta ga ƙoƙarin Gwamna Bassey Otu na sake lashe zaɓe a 2027.

Archibong ta sanar da matakin ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, inda ta ce ta yanke shawarar ne bayan tuntubar dattawa, iyalanta, al’ummar Kirista da kuma manyan masu ruwa da tsaki a siyasar jihar.

Ta bayyana cewa kishinta na yi wa al’ummar Cross River hidima ya fi muradunta na siyasa muhimmanci, saboda haka ta ga ya dace ta mara wa gwamnatin Gwamna Otu baya.

Haka kuma, ta gode wa shugaban NDC na jihar, Goddy Akwama, ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, John Odey, da sauran shugabannin jam’iyyar bisa damar da suka ba ta ta tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar.

Da yake mayar da martani kan ficewarta, Odey ya ce matakin ya ba shi mamaki, amma ya buƙaci mambobi da magoya bayan jam’iyyar su kwantar da hankulansu tare da nuna dattako.

Ya ƙara da cewa jam’iyyar na tattaunawa da shugabanninta da sauran masu ruwa da tsaki domin fahimtar dalilan matakin da Archibong ta ɗauka da kuma yanke shawarar matakin da ya dace, yana mai tabbatar da cewa NDC na nan daram kan burinta na gina Cross River mai ci gaban tattalin arziki.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *