Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta tabbatar da mutuwar ɗalibai huɗu, yayin da wasu shida ke kwance a asibiti sakamakon wani taron liyafa da aka gudanar a wani gida da ke wajen harabar jami’ar.

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Simon Ortuanya, ya ce ana gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya haddasa lamarin.

Ya bayyana cewa binciken farko ya nuna alamun da ke tayar da hankali kan yiwuwar shan barasa fiye da kima, da kuma kasancewar wasu kayayyakin da ake dangantawa da amfani da ƙwayoyi masu sa maye.

Farfesa Ortuanya ya ce jami’ar na haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin gano cikakken abin da ya faru da kuma tabbatar da dalilan da suka haddasa wannan iftila’i.

A matakin da ta ɗauka kan lamarin, jami’ar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku, tare da dakatar da dukkan harkokin zamantakewa da na karatu a wannan lokaci.

Hukumar jami’ar ta buƙaci ɗalibai da sauran al’ummar makarantar su kwantar da hankulansu, tare da guje wa yaɗa jita-jita ko hasashe yayin da ake ci gaba da bincike.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *