Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya amince cewa ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023 sun yi matuƙar rage amincewar ’yan Najeriya ga hukumar.
Amupitan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026, yayin wani taron tattaunawa a cibiyar Chatham House da ke Landan, inda ya buƙaci ’yan Najeriya su amince da jagorancinsa wajen gudanar da zaɓen 2027 cikin gaskiya da adalci.
Ya ce tun bayan hawansa muƙamin shugaban INEC a watan Oktoban 2025, hukumar ta ɗauki zaɓukan da ta gudanar a matsayin wata dama ta gano matsalolin da ke cikin tsarin zaɓe da kuma inganta ayyukanta.
- INEC za ta gwada na’urorin BVAS a faɗin Najeriya ranar 28 ga Nuwamba
- Majalisar Wakilai ta ware Naira miliyan 100 ga ’yan wasan Flamingos bayan lashe Kofin Duniya
A matsayin hujjar ci gaban da ya ce an samu, Amupitan ya ambaci zaɓukan gwamnonin Anambra da Osun, zaɓukan ƙananan hukumomin Abuja, zaɓen gwamnan Ekiti da kuma zaɓukan cike gurbi 16 na ’yan majalisu.
Shugaban ya ce a zaɓukan Anambra da Osun, waɗanda a baya ake ɗaukar kwanaki kafin kammalawa, an samu nasarar bayyana sakamako washegari.
Ya bayyana cewa rashin tsaro, matsalolin jigilar kayan zaɓe da sarrafa sakamako su ne manyan ƙalubalen da hukumar ke shirin tunkara gabanin zaɓen 2027.
Dangane da zargin da ake yi masa kan rashin nuna son kai, ya ce bai taɓa amfani da shafin X ba, kuma an miƙa batun ga DSS da Sufeto-Janar na ’Yan Sanda domin bincike.
Amupitan ya jaddada cewa biyayyarsa ga kundin tsarin mulkin Najeriya da dokar zaɓe ce, ba ga wani mutum ko wata ƙungiya ba.
Ya kuma yi kira ga matasa da su shiga harkokin dimokuraɗiyya tare da tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su, yana mai cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisar tarayya ranar 16 ga Janairu, 2027, sannan zaɓen gwamnoni da na ’yan majalisun jihohi ranar 6 ga Fabrairu, 2027.