Najeriya ta sake samun nasarar lashe zaɓen kujerar Majalisar Ƙungiyar Sadarwa ta Duniya (ITU), yayin taron ƙungiyar da ke gudana a birnin Doha na ƙasar Qatar.
Wannan nasara ta ba ƙasar damar ci gaba da kasancewa cikin majalisar ƙungiyar a wa’adin 2027 zuwa 2030.
Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ce ta jagoranci daidaita shigar ƙasar cikin taron, yayin da Ministan Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Zamani, Bosun Tijani, ya jagoranci tawagar Najeriya.
Jakadan Najeriya a Qatar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya kasance mataimakin shugaban tawagar, tare da Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), Aminu Maida, da tawagar wakilan dindindin na Najeriya a Geneva ƙarƙashin jagorancin Ambasada Innocent Imejuo.
- Shettima ya gabatar da matsayin Najeriya kan sake fasalin Majalisar Dinkin Duniya
-
Tinubu ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya
-
Amurka ta hana shugaban Sudan visa domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya
Haka kuma, jami’an Ma’aikatar Sadarwa, Hukumar NCC da ma’aikatan Ofishin Jakadancin Najeriya a Doha sun taimaka wajen wakiltar ƙasar a taron.
An kafa ƙungiyar ITU a shekarar 1865, kuma hedikwatarta na birnin Geneva da ke ƙasar Switzerland. Ƙungiyar hukuma ce ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da harkokin fasahar sadarwa da sadarwa ta zamani.
Ƙungiyar na da ƙasashe mambobi 194 da kuma sama da mambobin ɓangare daban-daban 1,000, waɗanda suka haɗa da kamfanoni, jami’o’i da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.
Najeriya ta shiga cikin ƙungiyar a shekarar 1961.