Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta buƙaci Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin cin tarar ƙungiyar kare haƙƙin jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (SERAP) Naira miliyan 100 bisa zargin ɓata sunan jami’anta biyu ta hanyar wallafa bayanan da hukumar ta ce ba gaskiya ba ne.
A nata ɓangaren, SERAP ta roƙi kotun da ta soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a kanta.
Sai dai kotun ɗaukaka ƙarar ta ajiye shari’ar domin yanke hukunci a wani lokaci da za ta sanar nan gaba.
- Kotu ta ji yadda aka yi garkuwa da jami’in DSS tare da kashe shi a 2022
-
Sowore ya zargi DSS da taimaka wa ’yan daba wajen kai musu hari a Ekiti
-
DSS ta gurfanar da mutum biyar kan sace ɗaliban NYSC 20 a Imo
Tun da farko, kotun da ta saurari shari’ar ta samu SERAP da laifin ɓata sunan jami’an DSS biyu da suka ziyarci ofishin ƙungiyar a ranar 9 ga Satumba, 2024.
Kotun ta ce ƙungiyar ta wallafa bayanan ƙarya da ke cewa jami’an sun kai samame ofishinta, lamarin da ta ce ya ɓata musu suna.
A hukuncin da ta yanke, kotun ta umarci SERAP ta biya tarar Naira miliyan 100 tare da wallafa saƙon neman afuwa a bainar jama’a ga hukumar DSS kan abin da ta aikata.