Wani jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa wasu mutane huɗu da ake zargi mambobin ƙungiyar IPOB ne suka yi garkuwa da jami’in hukumar, Ekpenyong Owoh, tare da kashe shi a watan Fabrairun 2022.
Jami’in binciken da aka gabatar a matsayin shaida ta farko (PW1), mai amfani da sunan ɓoye na AAA, ya bayyana hakan ne a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik yayin shari’ar waɗanda ake tuhuma huɗun.
Waɗanda ake tuhumar sun haɗa da Michael Okafor, wanda aka fi sani da Onyechimeleze; Chinedu Chukwudozie, wanda ake kira Kante; Chibunna Olisa da Chigozie Olisa, wanda aka fi sani da Ability.
An gurfanar da su a ranar 28 ga Satumba kan tuhume-tuhume shida da suka shafi ta’addanci da garkuwa da mutane, amma duk sun musanta aikata laifukan.
- Fiye da kashi 40 cikin 100 na masu ciwon sukari ba su san suna ɗauke da cutar ba
- Tinubu ya taya ɗansa murnar naɗa shi Dan Zaki na Masarautar Gwandu
Mai gabatar da ƙara ya zarge su da haɗa baki wajen aikata ta’addanci da yin garkuwa da Owoh a lokacin da yake tafiya daga Fatakwal ta Jihar Ribas zuwa Awka.
An kuma zarge su da kasancewa mambobin IPOB da ɓangaren mayaƙanta na Eastern Security Network (ESN), tare da mallakar bindigogi ba bisa ƙa’ida ba, ciki har da AK-47 da bindiga mai sarrafa harsasai.
Shaidar ta ce binciken da suka gudanar ya kai ga gano motar Toyota Pontiac da wayar marigayin, sannan aka kama Okafor da sauran waɗanda ake tuhuma.
Ya kuma yi zargin cewa Okafor, wanda ya bayyana a matsayin mataimakin kwamandan ESN, da sauran waɗanda ake tuhuma suna wurin lokacin da aka sace jami’in aka kai shi sansaninsu.
Bayan shaidar cewa waɗanda ake tuhumar suna da alamun ESN a jikinsu, kotun ta umarce su da cire rigunansu domin tantance hakan. Shaidar da lauyoyin kare waɗanda ake tuhuma sun tabbatar da kasancewar alamun.
Sai dai bayan lauyoyin sun yi zargin cewa an tilasta wa waɗanda ake tuhumar bayar da bayanansu, kotun ta umarci gudanar da shari’a ta musamman domin tantance ko sun bayar da bayanan ne bisa radin kansu, tare da ɗage sauraron shari’ar zuwa 16 ga Nuwamba.