Gwamnatin Tarayya ta ce za ta saki tanadin hatsi da kuma buhunan takin zamani miliyan uku a cikin wata guda domin ƙara yawan abinci a kasuwanni da kuma rage tsadar kayan masarufi a Najeriya.
Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026, inda ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na daidaita farashin abinci da tallafa wa manoma.
Ya ce za a fitar da takin ne ta hanyar shirin Shugaban Ƙasa na Samar da Taki, wato Presidential Fertiliser Initiative, domin sauƙaƙa wa manoma samun takin a lokacin noman rani.
- ADC ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da yunƙurin hana ’yan Najeriya bayyana ra’ayoyinsu ba
- ADC ta nemi Tinubu ya yi bayanin zargin biyan dala miliyan 4.5 ga wata Ba’amurkiya
Dangane da hatsi kuwa, ministan ya bayyana cewa gwamnatin za ta fitar da kayan abincin da ta saya tare da adanawa a ƙarƙashin shirin Guaranteed Minimum Price na Bankin Noma.
A cewarsa, fitar da waɗannan kayayyakin zai taimaka wajen ƙara wadatar abinci a kasuwanni da rage matsin lamba kan farashinsa.
Sai dai har yanzu gwamnati ba ta bayyana adadin hatsin da za ta saki ko takamaiman ranar fara raba shi ga jama’a ba.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar kayan abinci da kuma hauhawar kuɗin gudanar da noma.