Jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya bayani kan zargin biyan dala miliyan 4.5 ga wata Ba’amurkiya mai suna Diana London, wadda ake zargin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi amfani da ita wajen aikin hulɗa da ƙasashen waje.
Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta ADC (ADC-PCC), Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
ADC ta ce rahoton kashe irin wannan kuɗi abin damuwa ne, musamman a lokacin da ’yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki, rashin tsaro, yunwa da tsadar rayuwa. Sanarwar ta kuma yi zargin cewa an taɓa tuhumar London da laifin sata, kuma an same ta da laifi a jihar North Carolina ta Amurka.
- Tinubu ya taya ɗansa murnar naɗa shi Dan Zaki na Masarautar Gwandu
-
Tinubu ya taya jakadan Najeriya a Rasha murnar cika shekara 70 da haihuwa
Jam’iyyar ta buƙaci Tinubu ya bayyana wanda ya bayar da umarnin biyan kuɗin, asusun da aka cire su, ko kuɗin gwamnati aka yi amfani da su, da kuma irin ayyukan da aka ɗauki London domin gudanarwa.
Haka kuma, ADC ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) da Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya da su gudanar da bincike kan zargin tare da bayyana sakamakon ga ’yan Najeriya.