Lamarin ya faru ne a garin Atorkor da ke gundumar Anloga, a yankin Volta na ƙasar Ghana.
Rahotanni sun bayyana cewa kunkurun ta kauce wa hanyar komawa teku, inda ta shiga wani tafki da ke kusa da bakin tekun.
- ADC ta nemi Tinubu ya yi bayanin zargin biyan dala miliyan 4.5 ga wata Ba’amurkiya
- ADC ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da yunƙurin hana ’yan Najeriya bayyana ra’ayoyinsu ba
Bayan gano ta, ma’aikatan hukumar tare da taimakon al’ummar yankin sun yi nasarar jagorantar ta daga tafkin zuwa teku.
An dai samu nasarar mayar da kunkurun cikin teku ba tare da wata matsala ba, bayan ceton da ma’aikatan sashen kula da namun daji suka gudanar.