Shugaban ƙungiyar, Lai Omotola, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a yayin taron manema labarai a ofishin ƙungiyar da ke Maryland, Legas.
Ya ce za a gudanar da muhawarar a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja, domin bai wa ’yan takarar damar gabatar da manufofinsu da kare su a gaban ’yan Najeriya.
Omotola ya ce shirin zai ɗauki tsawon sa’o’i uku, wanda ya ƙunshe sassa biyar da za su bai wa ’yan takarar damar amsa tambayoyi daga ’yan jarida da sauran jama’a.
- Ana zargin sojoji sun mutu bayan haɗarin motar soja a Yobe
- Babachir Lawal ya ce Obi zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027
Ya bayyana cewa kowane ɗan takara zai samu mintuna biyar domin amsa tambaya, yayin da ’yan jarida za su samu mintuna biyu.
Gidajen talabijin na TVC, NTA, News Central, AIT, Arise da Channels na daga cikin waɗanda ake sa ran za su yaɗa muhawarar.
Ya ƙara da cewa za a bai wa masu sauraro damar yi wa ’yan takarar tambayoyi kai tsaye, yayin da sashe na ƙarshe zai kasance ta yanar gizo domin ’yan Najeriya da ke ƙasashen waje su shiga muhawarar.
Omotola ya kuma ce za a kafa kwamitoci biyar domin kula da shirye-shiryen taron, inda kowane ɗan takara zai iya zaɓar wakilai biyar da za su shiga kwamitocin.
Shugaban ƙungiyar ya jaddada cewa babu wata jam’iyyar siyasa da ke ɗaukar nauyin shirin, yana mai cewa PIG ce ke gudanar da shi da kuɗinta.
Ya ce manufar muhawarar ita ce bai wa masu zaɓe damar tantance manufofin ’yan takara, alkawuransu da salon shugabancinsu, tare da bayyana cewa ƙungiyar za ta yi ƙoƙarin ganin manyan ’yan takarar sun halarci taron.