Ana fargabar mutuwar wasu sojojin Najeriya bayan wata motar soja da ke ɗauke da jami’an rundunar 27 ta Task Force Brigade ta yi haɗari a jihar Yobe ranar Juma’a, 20 ga Nuwamba, 2026.

Rahotanni da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta sun ce motar na ɗauke da kusan sojoji 60 ne a lokacin da haɗarin ya afku da misalin ƙarfe 10:30 na safiya, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa sansanin samar da kayan aiki.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata a haɗarin ba, haka kuma ba a bayyana musabbabin faruwar lamarin ba.

Motar ta kasance ta rundunar 27 Task Force Brigade da ke Buni Gari, jihar Yobe, amma har yanzu ba a samu sanarwar hukuma daga rundunar sojin Najeriya kan lamarin ba.

Ana jiran ƙarin bayani daga hukumomin soji domin tabbatar da halin da sojojin da abin ya shafa suke ciki da kuma cikakken bayani kan haɗarin.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *