A cikin sanarwar da magatakardar majalisar, Catherine Ujong Ubi, ta fitar ranar 20 ga Nuwamba, ta ce waɗannan hukumomi na buƙatar bayyana gaban kwamitin domin kare kasafin kuɗin da suka gabatar na shekarar 2027.
- An ceto wasu 24 bayan kifewar jirgin ruwa a Bayelsa
- Makinde ya yi alƙawarin nuna wa jihohi da al’umma rawar gani a harkokin haƙar ma’adanai
Shugaban kwamitin kuɗi da kasafin kuɗi na majalisar, Hon. Cyril James Omini, ya bayyana damuwarsa kan gazawar wasu hukumomi wajen amsa gayyatar da aka yi musu, yana mai cewa zuwansu zai bai wa kwamitin damar tantance buƙatunsu na kuɗi da kuma binciken ƙididdigar kuɗin da suka gabatar.
Omini ya yi gargaɗin cewa duk hukumar da ta ƙi amsa wannan kira za ta iya rasa kuɗaɗen da aka tsara ware mata a cikin kudirin kasafin kuɗin 2027.
Ya kuma buƙaci hukumomin da abin ya shafa su halarci zaman na ranar Litinin tare da dukkan takardun kasafin kuɗinsu, domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana a tsarin kasafin kuɗin jihar.