Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bayelsa ta tabbatar da mutuwar mutum huɗu tare da ceto wasu 24 bayan wani jirgin ruwa mai ɗaukar fasinjoji ya kife a mahadar kogin da ke tsakanin al’ummomin Oweikorogha da Otuan, a Ƙaramar Hukumar Southern Ijaw ta jihar.

Sanarwar rundunar ta ce jirgin ruwan na cikin gida yana kan hanyarsa ne daga Ayama zuwa al’ummar Ukubie domin halartar jana’iza, lokacin da hatsarin ya afku da misalin ƙarfe 11 na safiyar Juma’a, 20 ga Nuwamba, 2026.

Waɗanda suka mutu sun haɗa da manya biyu da yara biyu, kuma an ajiye gawarwakinsu a ɗakin ajiye gawa na Asibitin Tarayya da ke Yenagoa.

Rundunar ta bayyana cewa an kai mutum 19 da aka ceto zuwa Asibitin Ayama, yayin da wasu biyar da suka samu raunuka daban-daban aka kai su Asibitin Family Care da ke Yenagoa domin samun kulawar likitoci.

Sauran fasinjojin da aka ceto kuma sun koma garuruwansu.

Bayan faruwar lamarin, ’yan sanda tare da masu aikin nutsewa daga al’ummomin yankin da sauran masu aikin ceto sun fara aikin bincike da ceto.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ajao Saka Adewale, ya kuma umarci sashen kula da harkokin ruwa na rundunar da ya tura jami’ai zuwa wurin domin ƙarfafa aikin ceto.

A halin da ake ciki, direban jirgin mai suna Omovie, wanda ba a san cikakken sunansa ba, ya tsere bayan faruwar hatsarin, yayin da aka kama manajan jirgin mai suna MV Bina domin gudanar da bincike kan musabbabin lamarin da kuma gano waɗanda ke da alhakin faruwar sa.

Kwamishinan ’yan sandan ya miƙa ta’aziyyarsa ga Gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri, da iyalan waɗanda suka mutu, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

Rundunar ta kuma gargaɗi masu tuƙa jiragen ruwa da su guji ɗaukar fasinjoji fiye da ƙima, su tabbatar da samuwar rigunan kariya daga nutsewa da kuma amfani da su, yayin da ta buƙaci fasinjoji su dage sai an bi ƙa’idojin tsaron sufuri a ruwa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *