Mai Shari’a Obiora Egwuatu ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa Suleiman ne ya samu mafi yawan ƙuri’u masu inganci a zaɓen fidda gwani na ADC, amma jam’iyyar ta sauya shi da Ribadu ba bisa ƙa’ida ba.
Rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ce Suleiman, wanda ɗan uwan tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ne, ya shigar da ƙara ne domin ƙalubalantar matakin sauya shi da jam’iyyar ta yi.
- ’Yan sandan Kano sun gargaɗi direbobi kan cunkoson ababen hawa a hanyar Wudil
- NAF ta shiga shirin haɗin gwiwar rundunonin sojin saman Afirka kan agajin gaggawa
A hukuncin da ya yanke ranar Juma’a, Mai Shari’a Egwuatu ya ce doka ba ta ba jam’iyya damar sauya ɗan takarar da ya lashe zaɓen fidda gwani ba, sai idan ya janye daga takarar da kansa ko kuma ya rasu.
Alƙalin ya bayyana cewa tun da Suleiman bai janye daga takarar ba kuma yana raye, matakin sauya shi da aka ɗauka ya saɓa wa doka, don haka ba shi da inganci.
Kotun ta umarci INEC da ta gaggauta mayar da sunan Omar Suleiman a matsayin halastaccen ɗan takarar ADC na gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2027.