Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta shiga shirin haɗin gwiwa da rundunonin sojin saman ƙasashen Afirka domin ƙarfafa matakan kai agajin gaggawa da ceton rayuka a lokacin ibtila’i da sauran matsalolin jin ƙai.

Rundunar ta bayyana cewa jami’anta sun halarci taron ƙarshe na tsara atisayen haɗin gwiwar rundunonin sojin saman Afirka (AAAF), gabanin gudanar da atisayen NGUVU PAMOJA 2027, wanda aka tsara gudanarwa daga 28 ga Janairu zuwa 3 ga Fabrairu, 2027, a biranen Nairobi da Kisumu na ƙasar Kenya.

Taron ya taimaka wajen kammala shirye-shiryen atisayen irinsa na farko a Afirka, wanda zai haɗa da amfani da jiragen sama wajen gudanar da ayyukan agajin jin ƙai da tunkarar ibtila’i.

Ana sa ran kusan jami’an soji 500 daga ƙasashe daban-daban za su shiga atisayen.

NAF ta ce shiga cikin wannan shiri na ƙarfafa ƙudurin Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, na inganta shirin ko-ta-kwana, ƙwarewar aiki da kuma bunƙasa haɗin gwiwar dabarun soja da sauran ƙasashen Afirka.

Atisayen NGUVU PAMOJA 2027 zai ba rundunonin sojin saman Afirka damar haɗa ƙarfi da ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan agajin gaggawa, musamman lokacin bala’o’i da ke buƙatar saurin kai agaji domin ceton rayuka da rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *