Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), Seyi Makinde, ya yi alƙawarin aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziƙi da hukumomin gwamnati domin rage talauci da kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya idan ya lashe zaɓen 2027.

Makinde ya bayyana hakan ne bayan halartar ibada a Dunamis International Gospel Centre da kuma cocin NKST da ke Abuja.

Ya ce zai tabbatar da ci gaba da ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar, domin samar da ingantacciyar rayuwa ga ’yan Najeriya da kuma ƙarfafa tsaro.

Ɗan takarar ya jaddada cewa gyare-gyaren da yake shirin aiwatarwa za su mayar da hankali wajen rage talauci da inganta ayyukan gwamnati.

Makinde ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a 2027, zai ba da fifiko wajen samar da tattalin arziƙi mai ƙarfi da kuma inganta tsarin hukumomin ƙasar domin amfanin al’umma.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *