Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ware naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma da bunƙasa harkokin noma, a wani shiri na ƙara samar da abinci da ƙarfafa noman cikin gida a Najeriya.

Mai magana da yawun Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC, Dele Alake, ya bayyana cewa Bankin Noma na Najeriya ya tallafa wa manoma sama da 500,000, yayin da Tinubu ya amince da ƙarin naira tiriliyan 1.5 ga bankin domin faɗaɗa tallafin kuɗi ga harkokin noma.

Alake ya ce shirin Renewed Hope Smallholder Support and Value Chain Fund mai naira biliyan 250 ya tallafa wa manoma a jihohi 16, ciki har da mata sama da 70,000, ta hanyar raba buhunan taki miliyan 2.5 da buhunan iri 300,000.

Ya ƙara da cewa shirin na naira biliyan 200 na tabbatar da mafi ƙarancin farashin amfanin gona ya sayi tan 170,000 na masara, shinkafa, dawa da rogo, domin kare manoma daga sayar da amfanin gonarsu a farashi maras kyau.

Sauran shirye-shiryen sun haɗa da tura taraktoci 1,571 zuwa jihohi 23, tallafa wa manoman citta 3,200 a Kachia ta Jihar Kaduna, da shirin naira biliyan 385 na samar da kayan aikin noma masu amfani da wutar lantarki, wanda ya haɗa da babura masu ɗaukar kaya 44,000 da famfunan ban-ruwa masu amfani da hasken rana 100,000.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *