Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ilimin Jami’o’i ya nuna damuwa kan zargin karya dokokin kundin tsarin mulki da wasu jami’o’in gwamnatin tarayya ke yi wajen ɗaukar ma’aikata da naɗa manyan jami’an gudanarwa.

Kwamitin ya buƙaci shugabannin jami’o’in su riƙa bin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, da kuma dokar Hukumar Kula da Daidaiton Wakilcin Ƙasa, domin tabbatar da adalci da daidaito wajen ɗaukar ma’aikata.

Ya ce sashe na 14(3) da 14(4) na kundin tsarin mulkin sun tanadi wakilcin jihohi da ƙabilu daban-daban cikin adalci a hukumomin gwamnati.

Wannan matsaya ta biyo bayan zaman sa ido da kwamitin ke gudanarwa, inda wasu jami’o’in gwamnatin tarayya daga yankin Arewa ta Tsakiya suka gurfana domin bayyana yadda suke gudanar da harkokin gudanarwa da ɗaukar ma’aikata.

Kwamitin ya jaddada cewa jami’o’in dole ne su tabbatar da gaskiya, adalci da dama daidai ga kowa wajen ɗaukar ma’aikata, maimakon barin bambancin yanki ko wasu muradu su rinjayi tsarin.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *