Tinubu ya yi wannan kira ne a yayin wani taron addu’a da iyalansa suka shirya masa a Yoruba Tennis Club da ke Legas ranar Lahadi.
Shugaban ya umarci Masari da ya koma Katsina domin sulhunta kansa da gwamnan da sauran waɗanda ake samun saɓani da su, yana mai cewa dole ne a kawar da fushi domin ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar APC.
- Shugaba Tinubu ya umarci Masari da Badaru su sasanta rikicin APC gabanin zaɓen 2027
- Tinubu ya ware naira biliyan 450 don tallafa wa manoma 500,000
Ya kuma miƙa irin wannan kira ga tsohon Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, da sauran shugabannin APC, inda ya buƙace su da su ajiye bambance-bambancen kansu domin tunkarar zaɓen 2027.
Tinubu ya jaddada muhimmancin haɗin kan jam’iyyar, yana mai kira ga shugabanninta da su yi aiki tare domin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.