Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da ke cewa ya janye daga takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2027, yana mai cewa har yanzu yana cikin fafatawar.

Daraktan Yaɗa Labarai na Yaƙin Neman Zaɓensa, Phrank Shaibu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce babu wani mutum ko ƙungiyar magoya baya da ke da ikon sanar da janyewar Atiku daga takara a madadinsa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce bai yanke shawarar janyewa ba, yana mai zargin cewa yaɗa labarin janyewarsa wani yunƙuri ne na raunana jam’iyyun adawa.

Atiku ya ce shirinsa na Affordable Life zai mayar da hankali wajen rage tsadar rayuwa, musamman hauhawar farashin abinci da sufuri da ke addabar iyalai a Najeriya.

Ya kuma buƙaci magoya bayansa su ci gaba da shirye-shiryen zaɓe tare da tabbatar da mallakar katin zaɓe na dindindin (PVC), yana mai cewa ’yan ƙasa ne za su yanke hukuncin wanda zai zama shugaban ƙasa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *