Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da shirin yi wa yara sama da miliyan biyu rigakafin cututtuka daban-daban, musamman cutar mashako, domin inganta lafiyar ƙananan yara a jihar.

Sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Nabilusi Abubakar K/Na’isa, ya fitar, ta ce shirin ya fara ne ranar Asabar, 21 ga Nuwamba, 2026.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa shirin zai shafi yara masu shekaru daga wata ɗaya zuwa watanni 59, a ƙarƙashin zagaye na huɗu na SARMAAN II da zagaye na biyu na Makon Kiwon Lafiyar Mata Masu Juna Biyu, Jarirai da Ƙananan Yara na shekarar 2026.

Ya ce shirin na tsawon kwanaki bakwai zai ƙunshi allurar rigakafin cututtuka daban-daban, rajistar haihuwar yara da kuma wayar da kan mata masu juna biyu kan muhimmancin zuwa awo.

Kwamishinan ya buƙaci iyaye da masu kula da yara su kai su cibiyoyin kiwon lafiya da wuraren da aka ware domin samun rigakafin, musamman na cutar mashako, da sauran ayyukan kiwon lafiya da shirin ya ƙunsa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *