Jam’iyyar PDP ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ta shiga haɗakar ƙungiyoyin adawa ta Coalition for Democracy, wadda tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa, Salihu Lukman, ke jagoranta, tare da bayyana cewa ba za ta halarci taron haɗakar da za a yi ranar 30 ga Nuwamba ba.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Jungudo Haruna Mohammed, ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a Abuja, inda ya ce PDP ba ta shiga wata yarjejeniya da haɗakar ba, kuma ba ta ba kowa izinin wakiltar ta a taron ko amincewa da duk wani mataki da za a ɗauka da sunanta ba.

Jam’iyyar ta ce haɗakar da ta amince da ita a halin yanzu ita ce Rainbow Coalition, wadda take samun goyon bayan jagoranta na ƙasa, Nyesom Wike.

Ta kuma bayyana waɗanda ake gabatarwa a matsayin wakilanta a haɗakar a matsayin mambobin da aka kora daga jam’iyyar, waɗanda ba su da ikon yin magana ko ɗaukar mataki a madadinta.

PDP ta ce waɗannan mutane sun sha faduwa a shari’o’in da suka shigar a Kotun Tarayya, Kotun Ɗaukaka Ƙara da Kotun Ƙoli, tare da zargin cewa kotuna sun hana Kabiru Tanimu Turaki, SAN, da abokan tafiyarsa bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar, sannan sun sanya musu tarar da ta haura naira miliyan 100 kan zargin amfani da kotuna wajen shigar da ƙarar da ba ta da tushe.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *