Tinubu ya bayar da umarnin ne a wajen taron addu’ar da iyalansa suka shirya masa a Legas, inda ya umarci mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabiru Masari, da ya koma Katsina domin sasanta kansa da Gwamna Dikko Umar Radda.
Haka kuma, ya buƙaci tsohon Ministan Tsaro kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Badaru, da ya taimaka wajen sasanta rikice-rikicen cikin gida na APC a wasu yankuna, yana mai cewa dole ne a kawar da fushi da bambance-bambancen da ke tsakanin shugabannin jam’iyyar.
- Tinubu ya ware naira biliyan 450 don tallafa wa manoma 500,000
- Makinde ya yi alƙawarin gyara tattalin arziƙi da ƙarfafa hukumomi idan ya zama shugaban ƙasa
Shugaban ya kuma buƙaci ’yan Legas su fito sosai a zaɓen 2027, tare da ƙarfafa magoya bayansa su tabbatar sun mallaki katin zaɓe na dindindin (PVC), domin samun isassun ƙuri’u da za su taimaka masa samun wa’adi na biyu.
Taron ya samu halartar gwamnoni, ministoci, shugabannin APC da malaman addinin Musulunci da Kirista, inda Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da tsohon Gwamnan Jigawa, Badaru, suka yi kira ga ’yan Najeriya da su mara wa Tinubu baya a zaɓen mai zuwa.
[…] Shugaba Tinubu ya umarci Masari da Badaru su sasanta rikicin APC gabanin zaɓen 2027 […]