Rundunar ta yabawa Dakarun ta game da jajircewa da suka nuna wajen ragargazar 'yan Ta'aadar

Wasu Yan Bindiga da ake kyautata zato yan Kungiyar Boko Haram ne, sun kai hari kan sansanin sojin Runduna ta 25 da ke yankin Mandaragirau a Karamar Hukumar Biu ta Jihar Borno.

Akalla Sojoji Biyar ne da ‘Yan Kungiyar Sa kai ta (Civilian Joint Task Force CJTF) guda Uku ne suka rasa rayukansu a harin, yayin da suke bakin aiki.

Cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai  na Rundunar  Laftanar  Kanar Haruna Sani ya fitar, ta ce dakarun da ke sansanin sun dakile harin duk da  rashin kyawun yanayi da rashin ganin hanya saboda ruwan saman da ake tafkawa.

Ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun kai hari kan sansanin ne da misalin karfe 3 na Asubahi, inda suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin wasu sassa na sansanin

“Dakarun mu sun jajirce wajen mayar da martani, sun dakile yunuƙurin kutsen ‘yan bindigar tare da jikkata da dama. Wannan ya nuna ƙarfin zuciya da juriyar dakarun mu a  Mandaragirau, kuma ya nuna ƙarfin gwiwa da ƙwazon ma’aikatanmu” in ji Sani.

A cewar sa, kasa cimma nasarar karbe iko da Sansanin na nuni yadda ‘yan ta’adda ke cikin matsanancin halin matsi, na neman Mafakar da zasu iya amfani da ita wajen tsantsanta hare-hare kan fararen hula.

Wasu majiyoyi a Karamar Hukumar Bi’u sun tabbatar da lamarin, na mamaye sansanin sojin  da yan ta’addar suka yi na kusan Sa’a guda, ba tare da samun nasarar karbe iko da shi ba.

Wani Shugaban wata Kungiyar Hadin kai ta Matasan Kudancin Borno mai suna  Samaila Kaigama, yace ‘Yan ta’addar sun kuma kai hare-hare  a wurare da dama a lokaci guda.

Kaigama ya yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙarfafa matakan tsaro da ƙarfafa haɗin kai da al’umma don inganta tattara bayanai kan motsin ‘yan ta’addar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *