Rashin mutuntawa ce ta sa na fice daga APC

Tsohuwar Sanatar Ogun ta Tsakiya kuma ‘yar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Farfesa Iyabo Obasanjo, ta yi murabus daga jam’iyyar APC.

Obasanjo, ta bayyana dalilanta na ficewa daga APC da suka hadar da rashin mutunta ta, kin amincewa da ita da kuma rashin adalci daga shugabannin jam’iyyar a Jihar Ogun.

Obasanjo, wadda kwanan nan ta nemi tikitin takarar gwamna na APC a Jihar Ogun, ta sanar da murabus dinta a cikin wata wasika mai kwanan watan 31 ga Mayu da aka aika wa shugaban APC na jihar, Cif Yemi Sanusi, kwafin wacce aka baiwa manema labarai a ranar Litinin.

A cewarta, duk da cewa ta yi alkawarin bin duk wani tsarin dan takarar maslaha da jam’iyyar ta dauka, amma ba a tuntube ta ba kuma ba a saka ta a cikin tsarin ba kafin a sanar da Adeola a matsayin dan takarar maslaha.

Ta kuma yi zargin cewa an hana wasu daga cikin magoya bayanta shiga wurin da aka bayyana dan takarar, sannan an yi musu barazana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *