Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) da takwararta ta ‘yan kasuwa TUC sun yi barazanar shiga yajin aiki matukar ba a dauki matakan gaggawa wajen magance matsalar tsaro da ke kara ta’azzara a fadin kasar nan.
Kungiyoyin sun bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a taron ranar Kwadago ta Duniya karo na 114, da ake yi a Birnin Geneva na kasar Switzerland.
Shugabannin kungiyoyin sun ce yawaitar hare-haren ta’addanci, ayyukan ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran munanan laifuka na ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya tare da kawo cikas ga harkokin tattalin arziki.
- Kotu ta haramta saya wa ‘yan majalisa motocin Naira biliyan 110
- Gwamnatin tarayya zata fara biyan kananan ’yan kwangila bashi
- Kotu ta haramta saya wa ‘yan majalisa motocin Naira biliyan 110
Yan kungiyar na nuna damuwa kan yadda ma’aikata da dama ba sa samun cikakken tsaro a wuraren aikin su, gidajen su da kuma kan hanyoyi, tare da jaddada bukatar gwamnati ta dauki kwararan matakai domin dawo da zaman lafiya.
Kungiyoyin sun yi gargadin cewa idan ba a samu gagarumin sauyi ba, za su shiga yajin aiki domin tilasta wa hukumomi daukar matakan da suka dace.
Kungiyoyin dai sun bukaci Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro su kara kaimi wajen yaki da matsalar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
