Hadin kan shiyyoyi zai taimaka wajen hana masu barna tserewa zuwa sassan kasarnan

Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya amince da tura Mataimakan Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (DIGs) zuwa shiyyoyin ƙasar nan.

Cikin wata sanarwa da hedikwatar Rundunar ta fitar, tace Babban Sufetan ya bayar da umarnin ne a a ranar Talata a Abuja, domin inganta harkokin tsaro da tabbatar da hadin kai tsakanin shiyyoyin.

Matakin na daga cikin ƙoƙarin rundunar na ƙara inganta ayyukan tsaro, ƙarfafa sa ido da jagoranci a matakin shiyyoyi, tare da tabbatar da saurin magance barazanar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

IGP Disu ya ce sabbin jami’an za su yi aiki kafada da kafada da Mataimakan Sufeto Janar da Kwamishinonin ‘Yan Sanda domin tabbatar da ingantaccen aiwatar da manufofi da tsare-tsaren tsaro.

Haka kuma, ya umarci dukkan Kwamishinonin ‘Yan Sanda na jihohi da su fara gudanar da ayyukan tsaro na haɗin gwiwa da jihohin maƙwabta a ƙarƙashin wani shiri da aka yi wa lakabi da “Sintirin Haɗin Kai.”

A cewarsa, masu aikata laifuka kan yi amfani da iyakokin jihohi wajen tserewa bayan aikata laifuffuka, saboda haka akwai buƙatar ƙarfafa musayar bayanan sirri, sadarwa da kuma haɗin gwiwar ayyukan tsaro tsakanin jihohi.

Ya kuma buƙaci kwamishinonin ‘yan sanda su riƙa gudanar da sintiri a manyan hanyoyin shiga da fita tsakanin jihohi tare da yin aiki tare domin dakile ayyukan masu aikata laifuka.

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da amfani da bayanan sirri, haɗin gwiwar hukumomin tsaro da dabarun aikin ‘yan sanda na zamani wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *