Barcelona ba za ta sayi Marcus Rashford ba a wannan bazara, yanzu haka Manchester United za ta iya sayar da dan wasan ga Bayern Munich kan kudi mai tsoka.
Kungiyar ta Catalonia ta yanke shawarar ba za ta yi amfani da zabin sayen dan wasan gaban ba, wanda ta rattaba hannu a bazarar da ta gabata da Manchester United a matsayin wani bangare na yarjejeniyar aro.
Da farko Barcelona na fatan ta dawo da Rashford, mai shekara 28, bayan zaman aro inda ya samu nasarar zura kwallaye 14 a duk gasannin da ya buka.
-
FIFA ta magantu kan hana alkalin wasa daga Afirka shiga Amurka
-
Super Falcons ta doke Teranga Lioness
Sai dai, bayan sayo Anthony Gordon da makudan kudade da kuma niyyar sake yin tayi ga Julian Alvarez, Barca ta yanke shawarar cewa amfani da zabin sayen Rashford na Yuro miliyan 30 ba zai musu ba.
“Barcelona ba za ta biya kudin Yuro miliyan 30 ba, don haka dan wasan zai koma kulob din Ingila,” a cewar wani rahoton Fabrizio Romano a shafinsa na X.