Gwamnatin Jihar Edo ta rufe makarantun sakandire guda uku zuwa wani lokaci saboda barazanar rashin tsaro.

Idan ba a manta ba, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) a Jihar ta nusantar da mahukunta boyayyen shirin garkuwa da daliban makaranta a wani bangaren Jihar ta Edo

A wata sanarwa, hukumar ta DSS ta ce bayanan sirrin da ta samu suna nuna cewa masu garkuwa da mutane suna shirin sace daliban makaranta musamman a shiyyar Edo ta Arewa.

Hakan ya sa Ma’aikatar Ilimi ta Jihar ta dauki matakin gaggawa na rufe makarantun zuwa wani lokaci.

Wata sanarwa da ta samu sa hannun Enodolomwanyi Otamere a madadin Ma’aikatar ta lissafo makarantun da abin ya shafa, wadanda suka hada da Ososo Grammar School da Ososo Comprehensive High school da Makeke Secondary School, duka dake Karamar Hukumar Akoko-Edo.

Sanarwar ta ce an dakatar da karantarwa ko aikace-aikace a makarantun har sai abin da hali ya yi.

Hakanan, dalibai da ke rubuta jarabawar kammala sakandire ta WASSCE za su ci gaba da rubuta jarabawar su tare da tsaurara masu tsaro a lokacin gudanar da jarabawar.

Kazalika, Ma’aikatar ta umurci shuwagabbanin makarantun sakandiren da su mika wa iyaye ‘ya’yan su sannan su tabbata da tsare kayan aikin makaranta, kulawa mai kyau.

Sanarwar ta kara da cewa shuwagabannin makarantu su kasance cikin tuntuban hukumomin Ma’aikatar Ilimi da jami’an tsaro lokaci bayan lokaci har zuwa lokacin da za a janye dokar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *