Shari’ar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Abubakar Sirika, ta bayyana a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa an yi amfani da wani jirgin kamfanin Ethiopian Airlines tare da yi masa tambarin Nigeria Air domin nuna kamar an ƙaddamar da kamfanin jirgin na ƙasa.

Shaidar, Christopher Odofin, jami’in bincike na EFCC, ya shaida wa Mai Shari’a S.C. Oriji cewa an kawo jirgin ne zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ranar 27 ga Mayun 2023, kwanaki uku kafin ƙarshen gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, sannan aka mayar da shi Addis Ababa ranar 29 ga Mayu.

A cewarsa, bincike ya nuna cewa an yi yarjejeniya da Ethiopian Airlines ne domin ajiye jirgin na tsawon kwanaki uku kawai tare da tambarin Nigeria Air, ba domin fara aikin kamfanin jirgin ba.

EFCC na tuhumar Sirika tare da ‘yarsa Fatima Hadi Sirika, surukinsa Hamma Jalal Sule da kamfanin Al Buraq Global Investment Limited da laifukan cin amanar ofis da karkatar da kuɗaɗen jama’a da suka haura naira biliyan biyu.

Shaidar ta kara da cewa an gano cewa an samu karin kudi a kwangilar kafa Nigeria Air da aka bai wa kamfanin Tianaero Nigeria Limited, daga Naira Miliyan 299 zuwa Miliyan 599 bisa umarnin Sirika.

Haka kuma, anyi bincike akan wani tsohon Babban Sakatare a ma’aikatar inda aka gano saƙon murya da ake zargin Sirika ya aiko daga kasar Spain yana umartar da a tabbatar an bai wa kamfanin Tianaero kwangilar.

Mai Shari’a Oriji ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 17 ga Yunin, 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *