Majalisar Wakilai ta amince da tsarin rundunar ƴan sandan jihohi, bayan amincewa da rahoton da aka gabatar mata kan shirin kafa rundunar.
An ɗauki wannan matakin ne yayin zaman majalisar na ranar Alhamis karkashin Shugabancin Honarabul Tajudeen Abbas, inda mambobin majalisar suka duba shawarwarin da nufin samar da cikakken tsaro a fadin Najeriya.
Wannan amincewa ta kafa babban tarihi a cikin daɗaddiyar muhawarar da ake yi kan kafa ƴan sandan jihohi, wanda masu ruwa da tsaki da dama suka daɗe suna fafutuka a kai. a matsayin mafita ga matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin ƙasar.
Masu goyon bayan tsarin na cewa rarraba ikon ƴan sanda zai inganta harkar tattara bayanan sirri, gaggauta ɗaukar mataki kan barazanar tsaro, sannan zai baiwa jihohi damar taka rawar gani wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Baya ga shirin kafa ƴan sandan jihohin, ƴan majalisar sun kuma amince da sassa 18 a cikin kundin tsarin mulki da za’a yi wa kwaskwarima, na shekarar 1999.
Sai dai kuma, waɗannan shawarwari za su buƙaci amincewar Majalisar Dattawa da kuma Majalisun Dokoki na Jihohi, kafin su zama doka cikakkiyar dokar da shugaban kasa zai rattabawa hannu.
