Majalisar Dattawan Najeriya ta fito fili ta nesanta kanta da sammacin kama tsohon Babban Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, wanda Kwamitin binciken asusun gwamnati na majalisar ya bayar a ranar Laraba.
Haka nan majalisar ta soki tare da nesanta kanta da kalaman Sanata Adams Oshiomhole, wanda a lokacin zaman kwamitin na ranar Laraba ya kwatanta kamfanin na NNPCL da “gungun miyagu da barayi.”
-
Kungiyoyin Fararen Hula sun yi zanga-zanga kan rashin tsaro
-
Majalisar Wakilai za ta yanke hukunci kan ‘yan sandan Jihohi
Haka nan Sanatoci da suka hadar da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, sun ja kunnen Oshiomhole da sauran sanatoci da su daina amfani da kalaman batanci ga ma’aikatun gwamnati da sunan Majalisar.
Ko da yake Oshiomhole ya kare kansa da cewa ya fadi kalaman ne cikin fushi saboda yadda jami’an kamfanin Mai na (NNPCL) din suka dade suna wulakanta sanatoci da kin amsa gayyatarsu ba tare da kwararan hujjoji ba.
Mele Kyari wanda yazu haka yake kasar jamus ya na jinya, da kansa ya aiko da takardar nuna bacin rai game da al’amarin, inda yake cewa bawai guduwa ya yi ba, ya sanar da majalisar halin da yake ciki tun a ranar 11 ga watan Mayu.
A zaman Majalisar na ranar Alhamis, Shugaban Masu Rinjaye Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar da kudiri na musamman don gyara lamarin domin kaucewa kwatanta haka anan gaba.
Majalisar ta bayyana cewa babu wani kwamiti guda daya da yake da ikon bayar da sammacin kama mutum har sai idan babban taron majalisar baki daya ya amince da hakan, shima da sa hannun Shugaban Majalisar Dattawa.
A karshe aka janye maganar kiran da aka yi wa Jami’an Tsaro su kama Mele Kyari da cewa babu shi a zahiri.
Majalisar na binciken Naira tiriliyan 210, da Ofishin mai binciken kudi na gwamnati ya gano cewar Kamfanin (NNPCL karkashin Mele Kyari bai shigar da su ba.
Sai dai Tsohon Babban Jami’in kudi a Kamfanin Umar Ajiya Isa, ya bayyanawa Majalisar cewa daukacin kudaden da (NNPCL) ya samu a duk tsawon shekarun nan triliyan ₦54.5 ne kacal, don haka ta yaya za’a ce Tiriliyan 210 sun bace?
