Majalisar Wakilai za ta kada kuri’a kan wasu muhimman kudurorin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa, ciki har da na kafa ‘Yan Sandan Jihohi.
Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin duba kundin tsarin mulki, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja.
A cewar Kalu, kudirin kafa ‘yan sandan jihohi na daga cikin manyan gyare-gyaren da majalisar za ta fara dubawa a zamanta na ranar Alhamis, domin samar da mafita ga matsalolin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar nan.
Benjamin Kalu da wasu ‘yan majalisa 14 suka mika kudirin gaban majalisar, na neman sauya wasu sassan kundin tsarin mulki domin bai wa jihohi damar kafawa da gudanar da rundunonin ‘yan sanda na kansu.
Masu goyon bayan kudirin na ganin hakan zai inganta tattara bayanan sirri, saurin kai dauki da kuma tsaro a cikin al’umma. Sai dai wasu na nuna fargabar cewa gwamnoni na iya amfani da rundunar wajen murkushe abokan hamayya na siyasa.
Idan majalisar ta amince da kudirin, zai tafi zuwa majalisun dokokin jihohi domin samun goyon bayan aƙalla jihohi 24 kafin a miƙa shi ga Shugaban Ƙasa domin rattabawa hannu.