Hukumar raya Babban Birnin Tarayya Abuja ta kaddamar da wasu sabbin tituna da ta yiwa lakabi da (Arterial No.5) akan Titin Obafemi Awolowo, da zai hada yankunan Dape da (Life Camp).
Da take jawabi a wurin bikin bude titunan, karamar Ministar Abuja Dakta Mariya Mahmood Bunkure, ta bayyana aikin a matsayin wani babban ci gaba ƙarƙashin tsarin (Renewed Hope) na Shugaba Tinubu.
Mariya Bunkure ta ce aikin yana nuna ƙudirin Shugaban Ƙasa na inganta hanyoyin sadarwa, bunƙasa tattalin arziki, da kuma kyautata rayuwar mazauna Babban Birnin Tarayya (FCT).
- Zanga-zangar Hausa a Birnin Ibadan
- Majalisar Wakilai za ta yanke hukunci kan ‘yan sandan Jihohi
- Sirika – Shaidu sun bayyana Yadda aka yaudari Al’umma da jirgin Ethiopia
Har ila yau, Karamar ministar ta yabawa Ministan Babban Birnin Tarayya, Barrista Nyesom Wike, wanda jagorancinsa ke kawo sauyi ga rayuwar Birnin.
Ministar tace da jajircewarsa ake samun ingantaccen sauyi a fasalin Abuja, ta hanyar aiwatar da muhimman ayyukan more rayuwa, da samar da ƙarin sauran damammaki ga mazauna Birnin.