Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauya sunan Cibiyar Nazarin Albarkatun Mai wato (Institute of Petroleum Studies) da ke Kaduna zuwa Jami’ar (General Shehu Musa Yar’Adua University of Geological Sciences and Engineering Technology).
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin jawabin da ya gabatarwa ‘yan ƙasa, domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta shekarar 2026.
Tinubu ya ce an yanke wannan hukunci ne domin girmama gudummawar da marigayi Shehu Musa Yar’Adua ya bayar wajen bunƙasar dimokuraɗiyya da ƙarfafa haɗin kan ƙasa a Najeriya
- ‘Yan Sanda sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su a Katsina
- Gobara ta tashi a wata kasuwa dake Kano
- An shiga jimami a Jami’ar Kebbi
“Daga cikin waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen gina dimokuraɗiyyar Najeriya ta zamani, muna girmama Janar Shehu Musa Yar’Adua saboda hangen nesansa na haɗin kai da haɗin gwiwar ƙasa,” in ji Shugaban
“Domin girmama irin gudummawar da ya bayar, Gwamnatin Tarayya ta amince da farfaɗo da kuma sauya sunan kammalalliyar Cibiyar Nazarin Man Fetur da ke Kaduna zuwa Jami’ar Kimiyyar Ƙasa da Fasahar Injiniya ta Janar Shehu Musa Yar’Adua.”
Marigayi Shehu Musa Yar’Adua, tsohon jami’in soja kuma fitaccen mai fafutukar dimokuraɗiyya, ya rasu a gidan yari a watan Disambar shekarar 1997 a lokacin mulkin marigayi Sani Abacha.
An tsare shi ne bayan an zarge shi da hannu a wani yunkurin juyin mulki da ake zargin an shirya wa gwamnatin wancan lokaci.
Yar’Adua shi ne babban ɗan’uwa ga marigayi Umaru Musa Yar’Adua, wanda ya shugabanci Najeriya daga shekarar 2007 har zuwa rasuwarsa a shekarar 2010.
