Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake rike da kofin gasar firimiyar Ingila, za ta fara kakar gasar firimiya ta shekarar 2026/27 a gida, inda za ta karbi bakuncin tawagar ‘yan wasan Coventry a ranar Juma’a 21 ga watan Agusta.
Ita kuwa Kungiyar kwallo kafa ta Liverpool, za ta ziyarci kungiyar kwallon kafa ta Newcastle a ranar Lahadi, 23 ga Agusta da misalin karfe 4:30 na yamma.
Yayin da kakar zata zo da sabon yanayi ga Kungiyar Man City ba tare da Pep Guardiola ba. Kungiyar zata bude wasan ta a filin wasa na Etihad da Bournemouth da misalin karfe 2 na rana ranar Lahadi 23 ga Agusta.
-
Gasar cin kofin duniya 2026: Mexico ta tsallake zuwa zagaye na Biyu
-
Vinicius ya ceci Brazil daga Maroko
Zakarun wasan share fage na Championship.
Hull City, za ta karbi bakuncin Manchester United a filin wasa na MKM a dawowarsu gasar firmiya da karfe 12:30 na ranar Asabar 22 ga Agusta, yayin da Ipswich za ta kara da Sunderland bayan matsayin da suka hau zuwa matakin Firimiya, wanda zai kasance da karfe 3 na rana.
A lokutan bukukuwan Kirsimeti dana Sabuwar Shekara kuwa, kungiyoyi za su samu akalla hutun sa’o’i 60 tsakanin wasanni kamar yadda sabon tsarin yazo dashi.
Wasannin karshe na gasar firimiya zai gudana ne a ranar 30 ga Mayu, 2027, dukkanin wasannin za su fara ne da misalin karfe 4 na yamma.
