Ministan yaɗa labarai da wayar da kai na Nijeriya, Mohammed Idris, ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su daina yaɗa ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a kafafen yada labarai da na sada zumunta, yana mai cewa yawan mayar da hankali kan ayyukansu yana taimaka wa manufar waɗanda ke son yaɗa tsoro da rashin zaman lafiya.
Da yake jawabi a wani taron koli kan tsaro da ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ) ta shirya tare da haɗin gwiwar hukumar tsaron farin kaya ta DSS, Idris ya ce dole ne ‘yan jarida su samar da daidaito tsakanin ‘yancin aikin jarida da kuma alhakin ƙasa domin ci gaban al’umma.
Ministan ya nuna damuwa cewa rahotannin kafafen yaɗa labarai kan fi ba da muhimmanci ga ayyukan ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, yayin da ake ba da ƙarancin kulawa ga ƙoƙari da sadaukarwar jami’an tsaro da ke kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
A cewarsa, aikin jarida mai nagarta ba ya nufin takaita ‘yancin faɗar albarkacin baki, sai dai yana buƙatar ƙwararrun ‘yan jarida su yi amfani da kyakkyawan tunani wajen tantance abin da ya kamata a ruwaito da kuma yadda za a gabatar da shi.
Ya ƙara da cewa mafi ƙwarewar ‘yan jarida su ne waɗanda suka san “abin da bai kamata a ruwaito ba domin amfanin gina ƙasa.”
Idris ya lura cewa Nijeriya na fuskantar ƙalubalen tsaro masu rikitarwa da suka haɗa da ta’addanci, tsattsauran ra’ayi, laifukan yanar gizo, yaɗa bayanan ƙarya da dai sauran su, lamarin da ya sa haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro ya zama mai matuƙar muhimmanci.
Ya jaddada cewa duka ɓangarorin biyu suna da muhimman rawar da suke takawa wajen gina ƙasa, inda hukumomin tsaro ke da alhakin kare rayuka da martabar ƙasa, yayin da kafafen yaɗa labarai ke aiki a matsayin masu sa ido da kuma zama gada tsakanin gwamnati da al’umma.
Ministan ya kuma yaba da yadda dangantaka tsakanin ‘yan jarida da hukumomin tsaro ke ƙara inganta, musamman DSS, yana mai cewa NUJ ta tabbatar da cewa babu wani rahoto na kamawa ko tsare ɗan jarida da hukumar ta yi cikin shekara ɗaya da rabi da ta gabata.