Kyaftin din Moroko, Achraf Hakimi

Kyaftin din Moroko, Achraf Hakimi zai fuskanci shari’a kan zargin fyade, kamar yadda masu gabatar da kara na Faransa suka tabbatar.

Wata mata mai shekaru 24 wadda ba a bayyana sunanta ba, tayi zargin dan wasan da yi mata fyade a gidansa da ke birnin Paris na kasar Faransa a shekarar 2023.

Ofishin mai gabatar da kara na jama’a dake  wani yanki a yammacin Paris ne, ya fara bincike na farko kan lamarin a watan Maris na 2023.

Kafafen yada labarai na Faransa sun ruwaito cewa Hakimi, mai shekaru 27, ya ki daukaka kara akan zarge zargen da akeyi masa.

Ko da yake tuni Hakimi, wanda zai jagoranci tawagarsa a wasan su na biyu na gasar cin kofin duniya da Scotland ranar Juma’a (karfe 11 na dare), ya musanta zargin.

“Na zabi yin shiru tsawon shekaru, na yi imani cewa kiyaye mutuncina, yin hakuri, da kuma amincewa da tsarin shari’a, zai ba da damar adalci a tsakani.” Hakimi ya rubuta a shafukan sada zumunta  ranar Juma’a.

lawyar mai gabatar da kara Rachel-Flore Pardo, ta bayyana cikin wata sanarwa cewar an shafe fiye da shekaru Uku ana shari’ar, kan zargin bata suna ga wadda take karewa.

Sai dai ba a kai ga sa ranar fara wannan shari’a ba tukuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *